Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Mawaki Dauda Kahutu RARARA-Kwamarade Sani Tela

Alfijr ta rawaito kwamarade Sani Bala Tela ya aikewa da Shahararren mawakin siyasar nan Dauda Kahutu Rarara wata wasika amma a bayyane.

Alfijr Labarai

Sani Tela ya fara da cewar, Da sunan Allah mai Rahma Mai jinkai gaisuwa mai yawa tare da fatan Alkhairi dafatan kai da iyali lafiya da sauran Al’amuran Rayuwa

Ya ƙara da cewa, na rubuto maka da wannan wasika ne domin na samu labarin abunda ke faruwa tsakaninka da kakanka mai girma gwamnan kano Dr Abdullahi Umar Ganduje.

A gaskiya na kadu sosai dajin wannan labarin, kuma nayi mamaki sabida a iya zamana da kai a matsayin makoci bansanka da rigima ba ko tashin hankali duk inda kake jama’a ne a kewaye da kai kuma abun hannun ka bai rufe maka ido ba.

Alfijr Labarai

Tela ya dora da cewa, kasancewar nasan ka ba sanin shanu ba, haka kuma na san wasu abubuwa na mutuntawa da darajawa irin na ‘da da Uba da ya gudana tsakaninka da kakanka, don haka bai kamata a yanzu kuma ace kai da shi haka na kasancewa ba, musamman a wannan yanayin da ake ciki na kowa na bukatar juna a cikinku.

Don haka Ina so na maka tuni, Allah ya yi maka tuni cewa, Allah yayi maka baiwa mai yawa kuma karka sa rai kuma zai barka ba tare da jarrabawa ba, don haka ka dauki wannan a matsayin jarrabawa.

Akwai mutane da yawa da suke neman dama irin taka basu samu ba kuma kar kamanta godiyar da zaka yiwa Allah shine, kayi kyakkyawar amfani da ita ta hanyar da ta dace sai Allah ya karo. In Ji Tela

Alfijr Labarai

Yana da kyau ka sani cewa Ita bukata ba koyaushe ake dacewa da ita ba, idan an dace ayi murna in an rasa a fawwalawa subhanahu wata’ala ayi hakuri akwai gobe.

Hakazalika duk abunda akace yana da waadi ai dadi gareshi, kwana nawa ya ragewa kakan naka ya karasa ya sauka inaga ba laifi bane idan anyi hakuri komài zai wuce.

Rarara kamun kai anyi shahararrun mawaka da yawa a kasar Hausa irin su Shata , Dankwairo, Dan Maraya da su abubakar Ladan wanda sabida dama da ya samu har jirgi aka saka shi akayi yawo dashi kasashen Africa don yazo ya wake Nahiyar, haka kaima watarana zaka zama tarihi ko da ranka ko ka mutu.

Alfijr Labarai

Don haka ina ganin ka samu karatun kur’ani daidai gwargwado to ya kamata kuwa kayi amfani dashi ta hanyar hakuri da yin sulhu da kakanka Ganduje kuma
masoyinka.

Sani Tela ya ƙara da cewar, ga shawarwarina kamar haka:-

1. Kayi kokari kayi takatsantsan da masu nuna maka goyon baya a yanzu don idan ta rikice ba zaka ga da yawa daga cikinsu ba sun arce su barka.

2. Ka kyautata kalamanka da lafuzanka a wakokinka kamar yadda addini ya umarta

Alfijr Labarai

3. Ka takaita abokan hamayya domin har naga anfara maka lissafin tsoffin gwamnoni da kuka samu matsala dasu

4. Ka ja kunnen masoyanka don wasu fitunune su ke rura wutar.

5. Kayi hakuri akan abunda aka maka na ba daidai ba

6. kabi kaidojin sana’arka da dokoki sai kazauna lafiya.

7. Kaci gaba da girmama magabata kaima sai a girmamaka

8. Alkharin da kakeyi ka toshe kunnenka ka ci gaba

9. Kaci gaba da bawa masu hakki hakkinsu duk sharrin mutum ya kyaleka

Alfijr Labarai

12. Sunan da kira Gwnonin uku dasu ka nemi su yafe maka har ga Allah a samu zaman lafya kuma idan an kira sulhu kada ka ki zuwa don Allah don Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam.

13. Ina da yakinin bazaka watsa kasa a ido don nasan kai mai jin shawarane

Maassalam

Daga Danuwanka

Camarade Sani Bala Tela

Alfijr Labarai

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *