Sanarwar ta fito ne a ranar Litinin cikin wata takarda da Abiodun Oladunjoye, Daraktan Ƙididdiga da Hulɗa da Jama’a na Fadar Shugaban Ƙasa, ya sanya wa hannu.
A cewar sanarwar, an dakatar da Umunubo daga mukaminsa, kuma ba ya wakiltar gwamnatin Tinubu a kowace irin mu’amala.
“An sanar da masu ruwa da tsaki a harkar tattalin arzikin dijital da na ƙirƙire a gida da waje, tare da jama’a gaba ɗaya, cewa Fegho John Umunubo, wanda a baya ya riƙe matsayin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Tattalin Arzikin Dijital da na Ƙirƙire (Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa), an sallame shi daga mukaminsa nan take,” in ji sanarwar.
Fadar Shugaban Ƙasa ta kuma yi gargadi cewa duk wanda ya ci gaba da yin hulɗa da Umunubo da sunan gwamnatin Tinubu, to da kansa yake.
“Duk wanda ya yi hulɗa da shi da sunan gwamnatin Shugaba Tinubu, to shi kaɗai zai ɗauki alhakin abin da ya faru. Muna shawartar duk masu ruwa da tsaki a harkar tattalin arzikin dijital da na ƙirƙire da su kiyaye wannan umarni yadda ya dace,” in ji sanarwar.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t