Wani Dan takarar Majalisa, Ya Tallafawa Al’Ummarsa Da Kuɗi Da Kofunan Shan Shayi

Alfijr ta rawaito Hon Adamu Ibrahim Na’ibbi (Yayaji) Dan takarar Majalisan cikin garin Potiskum ne a karkashin Inuwar Jam’iyyar People Democracy Party PDP a zaben shekarar 2023, yabada tallafi ga masu Saida Shayi mutane 70 a kwaryar Potiskum.

Alfijr Labarai

Na’ibbi yayi wannan tallafin ne domin tallafawa masu kananan sana oi a Mazaɓar da yake wakilta.

Tallafin ya kasance a kowane Ward an zabi mutane goma 10, in da ya bawa kowane ɗaya daga cikinsu Naira 5000, domin sukara jari a sana’arsu ta Shayi.

Sannan wadanda suka amfana da kudin an sake gwangwaje su da kofuna guda goma-goma domin bunkasa sana arsu ta shayin.

Yayin zaba wannan tallafi, Hon yayi kira ga matasa da su daina raina ƙaramar sana’a, domin daga karamar ne take zama babba.

Alfijr Labarai

Hon Yayaji ya roki wadanda suka amfana da tallafin da karsu kalli karancinsa, suyi amfani da shi ta yadda ya kamata

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *