Yadda Gidauniyar Dahiru Dawaki Ta Tabbatar Da Sakin Fursunoni 37 Albarkacin Ramadan

Alfijr

Alfijr ta rawaito wata kungiya mai zaman kanta a Kano mai suna Dahiru Dawaki Foundation ta nemarwa fursunoni 37 da ke da kananan laifuffuka a cibiyoyi biyar na jihar Kano yanci.

Shugabar kungiyar Hajiya Yasmin Dahiru Dawaki ta bayyana haka a lokacin da take zantawa da manema labarai a Kano.

Hajiya Yesmin Dawaki wadda ta kasance kwararriyace wajen harkar sana ar kwalliya da zayya, ta kuma Shahara wajen ayyukan jin kai don sanya farin ciki da annashuwa a fuskokin marasa galihu, musamman mata da yara.

Alfijr

Ta ce manufar kungiyar ita ce samar da ingantacciyar makoma ga mata da yara ta hanyar koyar da su hanyoyin dogaro da kai musamman ta na’ura mai kwakwalwa da kuma karfafa fasahar zamani.

Haj Yasmin ta ƙara da cewar, ina matukar bakin cikin ganin an daure mutane ciki har da mata saboda bashi da ake bin su, ta kuma kara Kira da masu hannu da shuni wajen hadin gwiwa da irin kungiyoyinsu don saka farin ciki ga al ummar Annabi musamman irin wannan lokacin ibadar azumi.

Cikin Fursunonin da suka sami shakar iskar yanci sun hada da Mata 16 da Maza 21,

Alfijr

Daga ƙarshe Haj Yasmin ta yi alkawarin ci gaba da irin wadannan ayyukan alherin, domin shine burinmu kuma shi muka saka a gaba.

A nasa bangaren Comrade Kabir Umar Dodo (KATUKAN MARADUN) mai bada shawara da tafiya tsakanin gudanar da ayyukan rage cunkoso a gidan yari na shekarar 2022 a jihar Kano ta Gidauniyar Dahiru Dawaki, ya bayyana jin dadinsa game da jajircewar shugabar gidauniyar Haj Yasmin, ya kuma kara kira da masu hannu da shuni da su tuntube su kan irin wadannan nan ayyukan daurarrun, domin akwai abin tausayi cikin.

Alfijr

Comrade Kabir yace zaka sha mamakin dan karamin kudin da bai taka kara ya karya Ba, don ana bin mutun bashi kaga an garkameshi tsawon lokaci.

Slide Up
x