Wani Hadarin Mota, Mutane Tara Sun Mutu , 10 Sun Jikkata A Abuja

Alfijr ta rawaito hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) ta bayyana cewa mutane tara ne aka tabbatar da mutuwarsu yayin da wasu 10 suka samu raunuka a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a hanyar Yangoji zuwa Abaji a babban birnin tarayya, Abuja.

Alfijr Labarai

Wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na Corps Bisi Kazeem, ya ce, hatsarin ya rutsa da wata mota kirar Toyota Hiace Bus mai lamba KTG-450 KQ da kuma motar Howo Sino a kan hanyar Yangoji zuwa Abaji da misalin karfe 6:05 na safiyar ranar Asabar.

Ya ce motar bas din ta fito ne daga jihar Osun yayin da ta nufi jihar Katsina amma abin takaici ta fada kan wata tirela da ke tsaye.

Ya jaddada cewa duka motocin da hadarin ya rutsa da su, motocin kasuwanci ne.

Alfijr Labarai

Kazeem ya ce, “Mutane 22 ne suka yi hatsarin. Dukkansu maza ne, mutane 10 ne suka jikkata sannan tara suka mutu, an kuma ba da agajin gaggawa ga mutane biyu.

Hukumar FRSC ta kwato N3,170, buhuna shida da kuma wayoyin hannu daban-daban guda 4.

“An ajiye gawarwakin mutane tara a babban asibitin na Kwali, kuma rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen Kwali ta dauki nauyin gudanar da bincike.”

A cewar Kazeem, Mukaddashin Rundunar Sojan Sama, Dauda Biu, ya ce hadurran sun samo asali ne daga wudun wuce gona da iri, daga bisani kuma aka rasa yadda za a shawo kan lamarin.

Alfijr Labarai

Biu ya lura cewa hadarurrukan da daddare sun fi kashe mutane fiye da yadda suke yi da rana.

Ya ci gaba da cewa rundunar za ta ci gaba da jan hankalin jama’a ta hanyar wayar da kan jama’a da har sai an samu nasarar da ake bukata.

Ya kuma bukaci masu ababen hawa da su tabbatar da cewa an tsara motocinsu kafin su dora su akan hanya domin gujewa hadurran hanyoyin musamman da daddare.

Slide Up
x