Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta kai farmaki a wata maɓoyar fitaccen sarkin ƴan ta’addan nan, Bello Turji, inda su ka lalata masa wurin ajiyar abinci tare da kashe daya daga cikin ‘ya’yansa.
Wani masani kan yaki da ta’addanci da tsaro a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya tabbatar da faruwar lamarin a wani sako da ya fitar a shafinsa na X a jiya Asabar, a cewar jaridar DAILY TRUST.
Makama ya ce harin da aka kai wa Turji da har zuwa yanzu ba a kai ga gano inda ya ke ba, ya faru ne sakamakon harin hadin gwiwa tsakanin sojojin kasa da na sama, a karkashin ‘Operation Fansan Yanma’, inda sojojin su ka tarwatsa maboyar ‘yan bindigar a Fakai, karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara, inda Turji da abokansa su ka dade suna gudanar da ayyukansu.
Majiyoyin sirri sun shaidawa makama cewa Turji ya samu gagarumar asara don an hallaka mayaƙan sa da dama.
“Mun kashe ɗansa da da yawa daga cikin mayakan sa a yayin farmakin. Na kuma saurari muryar Turji a firgice tana kira na neman ɗauki daga wasu shugabannin ƙungiyoyin ƴan fashin jeji guda bakwai kuma. abu ɗaya daga cikinsu da ya fito, kuma daya daga cikin ‘yan leken asirinsa ya tsira da kyar daga gare mu a yau,” in ji daya daga cikin majiyoyin.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj