
Alfijr ta rawaito wani ƙaramin soji ya hallaka wani babban janar na sojojin Najeriya da mota.
Lamarin ya faru ne a barikin sojojin Najeriya da ke unguwar Oshodi a garin Lagos.
Al amarin dai ya faru ne a kusa da barikin sojojin a lokacin da babban sojin ya fito daga wurin motsa jiki.
Kafar yada labarai ta PRNigeria ta ruwaito wata majiya da ta ce karamin sojin a buge yake da giya a lokacin da ya kade babban sojan.
Tuni dai aka tsare ƙaramin sojan a barikin domin gudanar da bincike
BBC Hausa
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai
https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ