Wani Magidanci Ya Rasa Ransa Sakamakon Faɗawa Rijiya A Kano

Alfijr ta rawaito Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ta tabbatar rasuwar wani Magidanci mai suna Malam Habibu Mu’azu mai shekaru arba’in da biyar 45, a garin ƴan Dutse da ke yankin ƙaramar hukumar Bichi.

Alfijr Labarai

Jami’in hulɗa da jami’a na hukumar Saminu Yusuf Abdullahi, ne bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema a ranar Juma’a.

Saminu ya bayyana cewa jami’an hukumar dake ƙaramar hukumar Bichi ne suka karɓi kiran gaggawa da misalin ƙarfe 07:44 na safe daga wani mai suna Malam Sanusi Abubakar inda ya sanar da su yadda bawan Allah faɗawa Rijiyar.

Ya kuma ce, “Bayan isar jami’anmu wurin da misalin ƙarfe 8:20 na safe, sun fito da shi ba ya cikin hayyacin sa, kuma bayan kai shi asibiti likita ya tabbatar da rasuwarsa.

Alfijr Labarai

Kakakin ya kara da cewa tuni hukumar mu ta miƙa gawarsa ga dagacin garin na Ƴan Dutse Malam Bello Usman, kuma muna ci gaba da binciken musabbabin faruwar lamarin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *