Wani Matashi Da Ya Yaga Qur’ani Da Taka shi! Ya Shiga Hannun Yan Sanda A Kano

Alfijr

Alfijr ta rawaito rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da damke wani matashin maigadi da ake zargi da yagawa tare da taka Al-Qur’ani mai girma.

Alfijr

Lamarin ya auku a ranar Lahadi a yankin Kuntau dake karamar hukumar gwale, kuma da kyar ya sha sakamakon yunkurin kone shi da jama’a suka yi.

Legit Hausa a shafinta na Twitter ta sanar wani ganau ya sanar da cewa ya tarar da jama’a da miyagun makamai za su halaka shi kafin jami’an Hisbah su kai dauki

Alfijr

Wanda ake zargin, ya kubuta daga babbaka shi da ranshi da jama’ar yankin Kuntau a birnin Kano suka yi niyya bayan isar jami’an hukumar Hisbah wurin.

Slide Up
x