Alfijr ta rawaito hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) ta ce mutane shida ne suka mutu sannan wasu shida suka samu raunuka a wani hatsarin da ya afku a unguwar Malam Tanko dake kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a jihar Neja.
Alfijr Labarai
Jami an runsunar sun kai wadanda aka gawarwakin wadanda suka rasu, zuwa babban asibitin Sabon Wuse kuma an mika motocin ga sashin ‘yan sanda da ke karamar hukumar Tafa,” inji shi.
Kwamandan ya dora alhakin faruwar hatsarin ne a kan gidan wuce sa a, da karkatar da hankali da kuma rashin tsaro direbobin
Ya shawarci masu ababen hawa da su yi taka-tsan-tsan tare da bin ka’idojin gudu don gujewa hadurra.
Alfijr Labarai
Jami’in kiyaye haddura ya ce, jami an za su ci gaba da sanya ido a kan masu amfani da hanyar don kiyaye tukin mota mai hatsari.