Farashin Kayayyaki Ya Kara Mummunar Tsada A Karon Farko Cikin Shekaru 17 A Najeriya.

Alfijr ta rawaito karon farko cikin shekaru 17, tsadar farashin kayayyakin masarufi ta karu da kashi 20.5 a Najeriya a cikin watan Agusta da ya gabata.

Alfijr Labarai

Raban da a ga irin wannan tashin goron-zabbi tun watan Satumban shekarar 2005.

Alkaluman da Hukumar Kididdiga ta Kasar NBS ta fitar a wannan Alhamis sun nuna cewa, adadin ya karu ne daga kashi 19.64 da aka gani a cikin watan Yuli.

Wannan al’amari ya haifar da tayar da jijiyoyin wuya a Najeriya wadda ita ce kasa mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afrika, yayin da babban bankin kasar CBN ya shiga cikin matsin lambar kara kudaden ruwa.

Alfijr Labarai

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da kokawa kan halin matsin rayuwa sakamakon tabarbarewar tattalin arzikin kasar.

Tabbar Yanci

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *