Alfijr ta rawaito wani mummunan haɗari ya lakume rayukan yan sanda uku da wasu mutum uku, bayan da suka ƙone ƙurmus a wata motar dakon kuɗi ta bankin Eco Bank a garin Argungu na Jihar Kebbi. Alfijr LabaraiKakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi, Nafiu Abubakar, ya bayyana cewar, wasu mutum biyar sun ji raunuka, uku daga ciki ‘yan sanda, lokacin da motar ta yi karo da wasu ababen hawa huɗu a kan titin Argungu zuwa Birnin Kebbi ranar Talata.Ya bayyana faruwar abin ne lokacin da mota ƙirar Carina E da ke ɗauke da jarkokin man fetur ke gudu saboda jami’an hukumar Kwastam na biye da ita daga Birnin Kebbi.Da isar motar ƙauyen Jeda, sai motar ta yi karo da motar dakon kuɗin kuma ta kama da wuta nan take wuta ta kama wasu motoci 3 ta kuma ƙone su ƙurmus. Alfijr LabaraiSanarwar ta ce motoci biyar ne da kuma babur ɗaya suka ƙone a hadarin da kuma mutum shida da suka mutu, ciki har da ‘yan sanda uku.Sa annan, mutum biyar, uku daga ciki ‘yan sanda, sun ji raunuka kuma an kai su asibitin Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Birnin Kebbi.”Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu aFacebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller