Rahotanni sunce anga mutumin rike da zabgegiyar adda yana ihu, yana mai cewa hayaniyar ibadar na damunsa,
Jaridar Alfijir Labarai Ta Rawaito an samu tashin tashina a wata coci da ke Jihar Abia, bayan wani mutum ya kutsa harabar cocin dauke da adda, yana zargin mabiya cocin da haddasa hayaniya tare da muzguna mishi cikin dare.
Lamarin ya faru ne a Ibeku, Umuahia, yayin da ake gudanar da ibadar dare (night vigil), inda mutumin da har yanzu ba a bayyana sunansa ba ya shigo cikin cocin dauke da adda, lamarin da ya tilasta wa masu ibada tserewa domin tsira da rayukansu.
Cikin wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, mabiya cocin na tsaka da yabo da rera wakoki ne lokacin da mutumin ya bayyana kwatsam.
Rahotanni sunce anga mutumin rike da zabgegiyar adda yana ihu, yana mai cewa hayaniyar ibadar na damunsa, tare da umartar su da su bar wajen.
Wannan lamari ya haddasa firgici da rudani, inda da dama daga cikin masu ibada suka rika gudu domin kare kansu. Zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a samu rahoton mutuwa ko rauni ba, kuma ba a tabbatar ko an kama mutumin ba.
Lamarin ya zo ne a daidai lokacin da ake samun karin koke-koke kan gurbatar muhalli ta fuskar hayaniya, musamman daga cibiyoyin addini, wuraren shakatawa na dare, masana’antu da kungiyoyi a fadin kasar.
A watan Mayun 2025, Hukumar Kare Muhalli ta Jihar Lagos (LASEPA) ta bayyana cewa ta karɓi korafe-korafe 1,616 kan hayaniya tsakanin Oktoba 2023 da zangon farko na shekarar 2025.
Korafe-korafen sun shafi cibiyoyin addini, mashaya, gidajen rawa, masana’antu da kungiyoyin waka. Hukumar ta ce ta dauki matakan hukunci a kusan lamura 610, ciki har da rufe wurare da kuma cin tarar masu laifin.
A ranar 18 ga Janairu, 2026, Gwamnatin Jihar Ogun ta rufe wata coci da ke titin Ima Road, Abiola Way a Abeokuta, tare da rufe wani shahararren wurin nishadi a Ota, bisa zargin haddasa hayaniya.
Haka zalika, Gwamnatin Jihar Anambra ta nuna damuwa kan hayaniyar ibadar coci da ke kawo cikas ga karatun dalibai a Onitsha. Kwamishiniyar Ilimi ta jihar, Farfesa Ngozi Chuma-Udeh, ta bayyana lamarin a matsayin abin damuwa yayin mayar da martani ga koken wata makaranta mai zaman kanta da ta koka kan hayaniyar cocin a lokutan karatu.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t