Wasu Ƴan Tiktok Sun Kwana Gidan Gyaran Hali Da Tarbiyya Bayan Bata Sunan Gwamna

Alfijr ta rawaito wasu matasa masu wallafa hotunan bidiyo a dandalin sada zumunta na Tiktok da Facebook sun kwana a gidan yarin Kano, bayan wata kotun majistare ta same su da laifin ɓata sunan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da ke Kano.

Matasan Mubarak Isa Muhammad, da Nazifi Muhammad Bala, sun yi fice wajen shirya gajeren bidiyon barkwanci, yawanci sukan kwaikwayon muryoyin wasu fitattun mutane ne.

Hukumar tace fina-finai ta jihar Kanon ce ta gurfanar da matasan a gaban kotun.

Takardar bayanan ‘yan sanda da aka gabatar a kotun ta nuna cewa matasan sun bayyana a wani bidiyo da aka yada a dandalin Facebook inda suka yi ikirarin cewa gwamnan jihar Kano baya kyalla ido a kan dukkan wani fili a jihar ba tare da ya sayar da shi ba.

Hakazalika a cikin bidiyon sun yi ikirarin cewa gwamnan mutum ne mai yawan bacci.

Lauyan da ya shigar da kara Barista Wada Ahmed Wada, ya shaida wa BBC cewa, na gurfanar da matasan gaban kotun saboda laifukan da suka hada da bata sunan gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da kuma kokarin tayar da fitina.

Ya Kara da cewa, matasan sun yi bidiyon ne a inda suka fito a matsayin malami da mai já masa baki inda suka rinka yi kamar suna karatu suna bata wa gwamnan suna a kan zarge zargen da suke cewa baya barin filayen a Kano da kuma yawan bacci.

Baristan ya ce wadannan laifuka ne ya sa aka gurfanar da su gaban kotu.

Kotun dai ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare matasan har zuwa ranar Litinin 7 ga watan Nuwambar 2022, don bayyana hukuncin da aka yanke matasan.

A nasa bangaren lauyan wadanda ake kara, Barista Anas Idiris Baba, ya shaida wa BBC cewa bayan karanta wa matasan abin da ake tuhumarsu sun amsa laifinsu.

Ba wannan ne karon farko ba da ake gurfanar da wani a gaban kotu kan tuhume-tuhumen yin batanci ga gwamnan na Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a dandalin sada zumunta.

Ko a farkon shekarar da 2022 ma, sai da kotu ta tsare wani tsohon kwamishina Ma’azu Magaji, bisa tuhume-tuhumen bata sunan gwamnan na Kano.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

BBC Hausa

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *