Alfijr ta rawaito ana zargin wani tsoho mai shekara 70 da wasu mutum biyu da yin fyade ga wata yarinya kurma mai kimanin shekara 13 da haihuwa a wani gidan burodi da ke gangaren kwadi a Tudun Wada, Zariya a jihar Kaduna.
Alfijr Labarai
Kurmar daliba ce ’yar aji shida na makarantar firamare, wacce tsofaffin suka yi ta mata fyade har zuwa lokacin da mahaifiyarta ta fara ganin wasu canje -canje a gabanta.
Wadanda ake zargi da aika aikar suna shekara 70, da shekara 60 da kuma mai shekara 50 mazauna Gangaren kwadi da ke Tudun Wada a Zariya.
Mai unguwar ta Gangaren Kwadi, Mallam Mohammed Danliti, da yake tabbatar da faruwar lamarin, ya ce bayan mahaifiyar Kurmar ta ga canji a gaban ‘yar ta ta, sa’ilin da take yawan cewa gabanta na ciwo, ta ce ta yi tsammanin ko keke ta hau ya haddasa mata da ciwon.
Alfijr Labarai
Ya kuma ce, “Sai daga baya da wata kawar kurmar ta sanar da mahaifiyar cewa tana ganin kurmar tana yawan zuwa gidan buredin ana ba ta kudi.
“Daga nan ne mahaifiyar ta dauko wuka ta kulle kurmar a daki ta yi mata kurarin za ta kashe ta in ba ta fada mata gaskiyar abin da ke faruwa ba.
“Nan ne kurma ta sanar da cewa mutanen suna yi mata fyade,” inji shi.
Mai unguwar ya ci gaba da cewa daga nan ne mahaifiyar kurmar ta dauko wuka ta zo ta shake mai gidan burodin, tana kokarin daba mashi, a lokacin ne a ka kira shi, inda ya kai su ofishin ’yan sanda na Tudun Wada Zariya.
Alfijr Labarai
Ya ƙara da cewar, yanzu dai duka mutum ukun suna hannun ’yan sanda inda ake ci gaba da gudanar da bincike a kansu.
Bayan binciken likitoci sun tabbatar da cewa tsofaffin sun lalata ta, kuma har sun shafa mata wani nau’in cuta.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb
Aminiya