Wata Budurwa Ta Nemi Yan Sanda Su Yi Mata Tsakani Da Saurayinta Dan Turkiyya, Saboda kisan Ummita

Alfijr ta rawaito bayan kisan da wani ɗan China, Geng Quanrong ya yi wa budurwarsa a jihar Kano, Ummukulthum mai lakanin Ummita, sai ga wata budurwa ta garzaya hukumar ƴan sanda kan a yi mata tsakani da wani saurayinta ɗan ƙasar Turkiyya.

Alfijr Labarai

Budurwar, wacce a ka sakaya sunanta sabo da tsaro, ta garzaya ne domin kai rahoton cewa ya matsa cewa sai ya aure ta, ita kuma ba ta so.

A cewar ta, kisan da Quanrong yai wa Ummita ne ya tsorata ta, shi ne ta yanke shawarar ta shigar da ƙorafi ga ƴan sanda domin ai musu tsakani.

Ta shida wa rundunar ƴan sandan cewa saurayin nata na da kishin tsiya da zafin soyayya, inda har ya taba daɓa wa kansa wuƙa a kan ta, inda ta ƙara da cewa har ma ta yi iƙirarin cewa idan har bata aure shi ba to wani abu zai iya faruwa da ita.

“Sakamakon haka ne nima na zo na shigar da ƙorafi sabo da abinda aka yi wa Ummita ya tsorata ni. Ya addabe ni yana ta bibiya ta.

Alfijr Labarai

Babu wani abu na kuɗi ko makamancin haka da ya taɓa shiga tsakanin mu amma ni ya matsamin in ji ta

Kakakin rundunar yan Sanda jihar kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce Kwamishinan Ƴan Sanda na Jihar, Abubakar Lawan ya bada umarnin a yi binciken ƙwaƙwaf a kan lamarin.

Ya kuma yi kira ga al’umma da su riƙa sanya ido da jajircewa a kan abubuwan da ke faruwa a tsakanin su.

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *