Wata Gobara Ta Ƙone Dukiya Ta Miliyoyin Naira Ta Kuma Lalata Wasu Abubuwa

Alfijr ta rawaito dukiyoyi na miliyoyin nairori sun kone bayan wata gobara da ta tashi a POWA Plaza, Jos road, Lafia, jihar Nasarawa.

A cewar wani ganau, gobarar ta tashi ne sakamakon wata tartsatsin wutar lantarki da ta tashi a daya daga cikin shagunan da misalin karfe 1 na safiyar ranar Talata 8 ga watan Nuwamba, 2022.

Ya ce gobarar ta kone mafi yawan kadarori a ginin da mallakar rundunar ‘yan sandan Najeriya ce, kafin jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Nasarawa su zo domin kashe gobarar.

Ya ce, “Gobarar ta fara ne da misalin karfe 1 na safiyar ranar Talata.

Gobarar ta kona kadarori na miliyoyin naira kafin jami’an kashe gobara su zo.

Har yanzu ba su iya kashe wutar gaba daya ba sai karfe 7 na safiyar yau inda suka kara tura wasu jami’an kashe gobara zuwa wurin.

Sama da shaguna bakwai abin ya shafa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *