Alfijr ta rawaito wata kotu ta amince da sammacin kama wani mutum da ake zargi da kashe matarsa da ‘ya’yansu maza biyu a gidansu da ke Gwangmyeong a birnin Seoul a ranar Juma’a.
Alfijr Labarai
Kotun gundumar Ansan ta yankin Suwon ta ce wanda ake zargin yana bukatar a tsare shi a hukumance, saboda fargabar cewa zai iya tserewa, saboda girman laifin da ya aikata.
Mutumin da ake zargi da kashe matarsa da ’ya’yansu matasa biyu, ya isa wata kotu da ke Ansan, kudancin Seoul, a ranar 28 ga watan Oktoba, domin halartar sauraran sammacin kama shi.
Wanda ake zargin, wanda aka boye sunan sa, an tsare shi ne a ranar Larabar da ta gabata, bisa zarginsa da kashe matarsa mai kimanin shekara 40 da ’ya’yanta maza biyu.
Alfijr Labarai
Daya daga cikin ‘ya’yan yana aji na tsakiya a makarantarsa, dayan kuma dalibin firamare ne.
Ya amince da aikata laifin ne a hanyarsa ta zuwa halartar sauraran sammacin kama shi a wannan kotu inda ya ce wa manema labarai, “Gaskiya ne na aikata wani laifi.” Sai dai kuma ya yi magana kan musabbabin aikata laifin da ya aikata, da alama yana dora laifin a kan wadanda abin ya shafa.
An ruwaito wanda ake zargin ya shaidawa ‘yan sanda cewa ya aikata kisan ne saboda rikicin cikin gida dake faruwa.
Wata majiya ta bayyana wanda ake zargin ya rasa aikin yi ne bayan ya yi murabus daga kamfaninsa kimanin shekara guda da ta gabata sakamakon rashin lafiya da ya yi fama da shi.
Alfijr Labarai
A cewar ’yan sanda da makwabta, mutumin da matarsa sun sha fama da rigima a aure a kan harkokin tattalin arziki da sauransu.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb
NAN