Wata Matukiyar Jirgin Sama ‘Yar Najeriya, Da Wasu Mutane 11 Sun Mutu A Hadarin Jirgin Sama

Alfijr

Alfijr ta rawaito wata ‘yar Najeriya, Adzuayi Ewuga, ta mutu a wani hatsarin jirgin sama a tsakiyar kasar Kamaru.

Marigayiya Adzuayi ‘yace ta biyu ce ga Sanata Solomon Ewuga, jigo a jam’iyyar PDP a jihar Nasarawa kuma tsohon karamin minista a babban birnin tarayya Abuja.

Rahotanni sun ce matukiyar jirgin ta mutu ne tare da wasu mutane 11 a cikin wani karamin jirgin sama mallakin kamfanin Caverton Aviation Kamaru, lokacin da ma’aikatan jirgin suka rasa hanyar sadarwa ta rediyo, lamarin da ya yi sanadin hatsarin jirgin.

Alfijr

Kafofin yada labaran kasar Kamaru sun rawaito cewa jirgin ya taso ne daga filin tashi da saukar jiragen sama na Yaounde Nsimalen zuwa Belabo da ke gabashin kasar, inda ya yi hatsarin da ya yi sanadin mutuwar dukkan mutanen da ke cikinsa.

Caverton Aviation Kamaru wani reshen ne na Caverton Offshore Support Group da ke Lagos Najeriya, wanda kuma ke sarrafa Caverton Helicopters.

Alfijr

Slide Up
x