Wata Mummunar Gobara Ta Lakume Gini Mai Hawa 35, Dake Daf da Burj Khalifa Na Kasar Dubai

Alfijr ta rawaito wata Mummunar Gobara ta tashi a wani bene mai hawa 35 a Dubai kusa da Burj Khalifa, gini mafi tsayi a duniya da sanyin safiyar Litinin din nan.

Har yanzu dai ba a san musabbabin tashin gobarar ba.

Jaridar Daily Mail ta bayyana gobarar ta fara ne da misalin karfe 2:20 na safe, kafin ta bazu cikin shingen, wanda ke cikin hadadden hasumiya mai suna 8 Boulevard Walk, wanda kamfanin Emaar mai samun goyon bayan gwamnati ya gina.

Hotunan ban mamaki sun nuna yadda wuta ta mamaye duk kusurwar ginin daga sama zuwa kasa.

Jami’in kashe gobara wajen sun sami nasarar kashe ta misalin karfe 3:45 na safe.,amma da safiyar yau ne aka ga wutar na kara ruruwa ginin.

Kamfanin dillancin labaran ya ruwaito cewa har yanzu hukumomi ba su tabbatar da ko wani ya samu rauni ba.

Wannan dai shi ne na baya bayan nan a jerin gobarar da ta tashi a hasumiya a birnin Dubai na kasar a shekarun baya-bayan nan, lamarin da ya sake farfado da tambayoyi kan amincin gine-gine da kuma rigar da ake amfani da su a kasar.

A jajibirin sabuwar shekara ta 2015, wata gobara ta cinye Address Downtown, daya daga cikin manyan otal-otal a Dubai, kuma kusa da Burj Khalifa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *