Yadda Jami’an DSS Dana Amurka Suka Kama Wasu Ƴan Ta’adda A Birnin Tarayya Abuja

Alfijr ta rawaito Adewale Adenaike, shugaban kamfani na 3, Trademore Estate, babban birnin tarayya (FCT), ya bayyana yadda jami’an hukumar tsaron farin kaya (DSS) da wasu sojojin Amurka suka kama wani wanda ake zargi da ta’addanci a cikin al’ummarsa.

Alfijr Labarai

Adenaike ya ce jami’an tsaron sun rufe kofar gidajen ne a ranar Litinin domin dakatar da zirga-zirgar ababen hawa.

Shugaban al’ummar ya ce jami’an sun sanar da shi cewa suna bin wani dan unguwar da ake zargi da “ayyukan ta’addanci”.

“Lamarin ya faru ne a ranar Litinin, muna cikin gidajenmu aka kulle dukiyarmu, babu mai fita, babu mai shigowa cikin estate.

Ya kara da cewa a matsayina na shugaba, na fito ne don jin abin da ke faruwa a cikin estate din, nan dai na gano cewa wani hari ne da jami’an DSS din da wasu sojojin Amurka suka yi, kuma an yi zargin cewa, wai suna neman wanda ake zargi da ta’addanci,” in ji Adenaike.

Alfijr Labarai

“Lokacin da nake zuwa bakin gate zuwa titina, sai jami’an DSS da suka rufe fuska suka hana ni zuwa, na ce musu ba zan iya tsayawa ba saboda mutane suna kirana don neman bayani don haka za su bukaci su fada min dalilin da ya sa ka zo nan, kuma ta haka ne na san aikin ta’addancin da ake zarginsa da shi. In Ji shi.

Ya kara da cewa, Saboda su DSS ne kuma tare da sojojin Amurka babu abin da zan ce, sai kawai na ce lafiya, sai sun yi abin da ya kamata su yi, kuma da suka gama abin da suke yi, sai muka ga sun kora wasu mutane biyu daga gidan.

“Yayin da nake magana da ku, ba ni da cikakken bayani game da abin da ya faru, ban san abin da ya faru ba.

An yi ta zage-zage da jita-jita, dake ni ba mai yada jita-jita ba ne, don haka na ki kara ta’azzara jita-jitar da nake ji.”

Alfijr Labarai

Adenaike ya ce jami’ansu sun kama wanda ake zargin ne a wani rukunin maza na wani gida biyu da wani dangi ke zama a gidan.

Peter Afunanya, kakakin hukumar DSS, bai amsa kiran da aka yi masa ba domin neman karin bayani kan lamarin.

A baya-bayan nan ne dai kasashen Amurka
da Birtaniya suka fitar da shawarwarin gargadi kan tafiye-tafiye na ƴan kasarsu da ke zaune a Najeriya game da yiwuwar kai hare-haren ta’addanci a babban birnin tarayya Abuja.

A ranar Lahadin da ta gabata, ofishin jakadancin na Amurka ya ce akwai karuwar hare-haren ta’addanci a babban birnin tarayya Abuja

Alfijr Labarai

Hakazalika ya yi gargadin tafiye-tafiyen da ba dole ba. Kwanaki biyu bayan haka, ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar da kwashe ma’aikatan “marasa gaggawa” da ‘yan uwansu a Najeriya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

THE CABLE

Slide Up
x

4 Replies to “Yadda Jami’an DSS Dana Amurka Suka Kama Wasu Ƴan Ta’adda A Birnin Tarayya Abuja

  1. Wannan gaskiya ne shi ne ka’idar labarai.wannan labari ne Mai taka tsan-tsan Allah Kara daukaka da sutura.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *