Yadda Kasuwar Cryptocurrency Ta Duniya Ta Sauka A Yau Litinin 21/02/2022

Alfijr

Alfijr ta rawaito Sadeeq Spikin na bayanin yadda kasuwar Cryptocurrency ta duniya ta sauka da kimanin kaso 1.69% yayin da adadin dukiyar da akayi investing a chikin ya dawo Dalar Amurka Trillion 1. da billion dubu dari takwas wato $ 1.803,205T.

Alfijr

Farashin Bitcoin ya sauka daga $44,204 zuwa $37,209 kimanin kusan $7000 ce ta ragu akan price da kasuwar ta bude dashi a satin da ya gabata.

Lokachin da jumullar Kudaden da ake hada hada dasu a Kasuwar yakai kimanin $2.082 kafin saukarsa zuwa yanzu.

Alfijr

Wannan kuma ya samu asali ne sanadiyar yaki ko kuma cacar bakin da yake faruwa tsakanin kasar Russia da maĆ™ociyarta ta UKRAINE Wadannan kasashe suna dauke da jumullar kaso 25 na al’ummar da kamfanonin da suke hada hadar kudi a Kasuwar Cryptocurrency ta duniya.


Coinmarketcap da Coigecko sun rawaito cewar farashin din

BTC Yana kan $37,857
Ethereum yana kan $2,635.99
BNB yake kan $369,72
XRP yana kan Price $0.7544
ADA yana kan $ 0.9200
Yayin da SOL Yake kan Price $87

Alfijr

Wadannan manya hajjoji na kasuwar sunyi faduwa kasa tun watan 12 na Shekar da ta gabata Yadda kowannensu yake akan kaso hamsin ko akasin haka na tsohon price dinsa.

Sadeeq Spikin
Cryptocurrency Analyst.

Slide Up
x