Zuba Jami’an Tsaro a Dazuka Zai Magance Matsalar Tsaro a Najeriya! Inji Detective Auwal Bala D/iya

Alfijr

Alfijr ta rawaito Detective Auwal Bala Durumin Iya fitaccen masanin tsaron nan ya bayyana cewa babban abun da gwamnati za ta fi mayar da hankali domin dakile ta’addanci shine samar da jami’an tsaro a dazukan ƙasar nan, duba da yadda ‘yan bindiga suke mamaye cikin daukan.

Alfijr

Detective ya bayyana haka ne a wajen taron kungiyar masoya Malam Muhammad Sunusi II, wanda aka gudanar a ranar Asabar din da ta gabata.

Ya kuma kara da cewa, Muhammadu Sunusi II ya rage kaso 80 cikin dari a fannin sha’anin tsaro ta hanyar samar da hanyoyin dena yawo da kudi a aljihu, da ajiyar kudi a cikin gidaje, shi yasa fashi da makami ya ragu sosai.

Alfijr

Kwamared Usman Aminu Sulaiman wanda shine shugaban kungiyar na kasa ya yiwa wakilin DM news karin haske akan makasudin shirya wannan taro.

Ya ce “Daga cikin abun da muka fi mayar da hankali shine tallafawa marayu da marasa karfi musamman lokutan azumi domin koyi da jagoran mu Khalifa Muhammadu Sunusi II” a cewar sa.

Alfijr

Yayin taron an gudanar da yiwa kasa addu’a karkashin jagorancin wakilin babban Malami na Madabo Sheikh Abubakar, tare da jawabai daga masana a fannin sha’anin tsaro.

Slide Up
x