Yadda Kungiyar Fm Charity Ta Fitar Da Daurarru Daga Gidan Gyaran Hali Da Tarbiyya Mutum 6

Alfijr ta rawaito kungiyar Friends of Mine charity initiatives tayi wani yunkurin alheri irin wanda ta saba yi lokaci zuwa lokaci

Ziyarar da kungiyar ta kai gidan gyaran hali da tarbiyya na gwauron dutse a ranar Lahadi, sun sami nasarar fitar da mutane 6 da aka kulle su akan bashin kudade kimanin Naira dubu dari da asirin da biyu, ₦122 000, Maza 4 matan aure 2 cikinsu har da mai goyo

Alfijr

Cikin abubuwan da kungiyar ta kai musu gidan gyaran halin sun hada da ruwan sha na leda 20, sai dunkulen girki kwali daya, sai Burundi guda 100.

Da yake jawabi a adamadin Controller na gidan gyaran halin mataimakin Controller Abdullahi Ibrahim (DCC) na gwauron dutse ya yaba da kokarin kungiyar matuka, sannan kuma kara kira da sauran kungiyoyi da suyi koyi da irin wannan kokarin

Alfijr

Shugaban kungiyar Abbas Musa SAS yace sun zabi wadannan mutanen ne duba da karancin kudaden da ake bin su, sannan kuma ga matan aure har da goyo, wannan ya ja hankalinsu wajen samar musu yanci

Ya kara daa cewar irin wannan aiki shine abinda kungiyarsa ta saka a gaba, kuma ya kara kira da masu hannu da shuni da masu mulki su taimaka kungiyar wajen cigaba da yada ayyukan alheri a fadin jihar Kano da kasa baki daya.

Alfijr

Suma wadanda suka shaki iskar yancin, sun yi godiya ga Allah sannan wannan kungiyar da ta fitar da su, domin suyi azumin watan ramadana a gidajensu