Yadda Wani Dan Majalisa Ya Ragargaza Gidan Radio Kano A Shekarar 1980

A rana irin ta yau: Satumba 20, 1980 Hon. Labaran Tanko ya ragargaza Radio Kano, saboda bayar da sanarwar ƙarya ga Malam Aminu Kano.

Alfijr Labarai

A ranar 20 SEP 1980 dan majalisar tarayya mai wakiltar Kano ta tsakiya kuma Jami in yaɗa labarai ta jam iyyar PRP ta Kano wato Hon Labaran Tanko, ya ragargaza gidan radiyo Kano.

Tarihi tv ta bayyana cewar ya gai ziyara ne

Yayin ziyarar ne yaga wata takardar sanarwar cewar wai an dage dawowar Mal Aminu Kano kuma jagoran jam iyyar daga London, kuma takardar na ɗauke da saka hannun M T Liman wanda shine a mazaunin sakataren Malam din.

Hon Labaran Tanko ya a gargadi editan da ke tace labarin da cewar, wannan takardar ta karya, ce kuma saka hannun na bogi ne.

Alfijr Labarai

Dai dai wannan lokacin ne rikici ya barke tsakanin gwamnonin jam iyyar PRP da kuma shugancin jam iyyar karkashin Mal Aminu Kano.

Hakan ta sa ake tunanin idan Malam ya dawo ya dauki mataki mai tsauri kan gwamnan Kano na wancan lokacin Abubakar Rimi da kuma gwamnan Kaduna Balarabe Musa.

Kan wannan dalilin ne Hon Labaran Tanko ya bukaci gidan radiyo Kano da su kaucewa rikicinsu na cikin gida.

Labaran karfe 8 na dare radiyo Kano suka saka labarin, nan fa Hon ya tuko motarsa daga gida a fusace bai zame ko ina ba sai dakin watsa Labaran, isarsa an fara shirin Jatau na Albarkawa, bai yi kasa a guiwa ba sai ya kama tunbuke wayoyin dakin da ragargaza kayan dake dakin watsa Labaran gaba daya, kuma yayi tafiyar sa abinsa.

Alfijr Labarai

Bayan tafiyarsa sai ma aikatan gidan suka sanarwa shugaban gidan Alh Badugu Bidda, nan take shi kuma ya kira ƴan sanda don su bi masa Hakkinsa.

Duk da wannan sanarwar Malam Aminu Kano bai fasa dawo daga London a ranar ba.

Yan sanda sun yi bincike kan ɗan majalisar, bayan kammalawa ne suka yi shiru abin su ba tare da daukar mataki ba, saboda sun gano takardar sun gano takardar da radiyon ta bogi cewa, kuma daga gidan gwamnatin Kano aka kitsa takardar.

Tarihi Tv

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *