Yan Karota Sun Sake Kama Mai Adaidaita Sahu Barawon Waya A Kano

Alfijr ta rawaito hukumar dake kula zirga zirgar Ababan hawa ta jihar kano KAROTA ta sake samun nasarar Kama Wannan matashin mai Suna Abdullahi Babakura Wanda a kwanakin baya Hukumar ta kamashi da laifin satar wayoyin mutane ta hanyar amfani da Babur din Adaidaita Sahu.

Jami’an na Hukumar ta KAROTA dai sun kara samun Nasarar chafke Wannan Matashine Akan titin kundila dake titin zari’a Road da ke Kano, yayin da wani matashi Mai suna Abdullahi Isyaku ya hau Babur dinsa domin kaishi Kano Guest-In.

Tun a Wancen lokacin jmi’an na ‘yan sanda suka kaishi gaban kuto a inda aka yankemasa hukuncin dauri ko biyan Tara.

Alfijr

A wannan karonma Hukumar ta KAROTA takara damka Babakura gaban ‘yan Sanda dan fadada Bincike da daukar mataki na gaba.

Kamar yadda kakakin Yaɗa Labaran hukumar Ayuba Jarimi ya fitar a ranar Litinin

Slide Up
x