Yan Kurkura sun gudanar da zanga-zanga a ofishin Karota a Kano

IMG 175723 19825 1755622677033

Wata Tawagar masu motar Kurkura sun gudanar da zanga-zanga a bakin ofishin Karota dake Kofar Nassarawa a yau Talata.

Yan ƙurƙurar sun tare hanyar dake zuwa titin Obasanjo karkashin Gadar sama ta kofar Nassarawa inda suke ta neman gwamnati ta kawo musu dauki kan gashin kumar da suka ce hukumar Karota na yi musu

A tattaunawar Alfijir labarai da Nasiru Muhd sakataren kungiyar yan Ƙurƙura ta jihar Kano yace sun fito wannan zanga-zanga zangar ne saboda wata sitika da aka kara kakaba musu ba gaira ba ɗa dalili.

Ya kara da cewar an yi musu sitika ta kwali wata 8, a baya suna kuma siya! Sai kuma yanzu aka kara kirkiro musu karin wata wai ita GTB! Kuma mu ba ko ina muke zuwa ba aikinmu baya wuce cikin garin Kano, kuma ace sai mun sake siyan wannan akan dubu 8, bayan wannan.

Don haka muke kira da Mai girma Gwamna Alh Abba Kabir Yusuf da ya kawo mana ɗauki idan kuma ba so ake mu koma masu zaman banza ba.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *