Alfijr
Alfijr ta rawaito alhazai daga kasashe da dama, ciki har da Najeriya, sun tsinci kansu cikin wannan hali na tsaka mai wuya, saboda cinkoson da aka samu a bangaren tashin matafiya na filin jirgin, saboda abin da suka kira fitowar matafiya fiye da sa’a 12 gabanin tashinsu.
Lamarin dai ya shafi wasu kasashen Afrika, ciki har da Najeriya, abin da ya sa wasu suka koka saboda yawancinsu duk guzuri ya kare.
Alhaji Abubakar, ya je Umrah ne daga jihar Kano a Najeriya, kuma yana daga cikin wadanda wannan mataki ya shafa, ya shaida wa BBC cewa bayan sun kammala Umrarsu, yanzu fitowa daga kasa mai tsarki ita ce matsala.
Alfijr
Ya ce” An samu tsaikon jigilar mutane zuwa gida ne saboda rashin tsari a kan yadda za a rinka kiran alhazan daya kamata su tashi zuwa gida, abin da ya janyo filin jirgin saman na Jeddah ya dinke da alhazai.
Alhaji Abubakar ya kara da cewa ba a tsara abin ba ne ta yadda jirage suna kwasa ana fitarwa, abin da ya janyo filin jirgin saman ya cunkushe.
Alfijr
Shima Alhaji Sa’idu Makwarwa daga Kaduna, ya shaida wa BBC cewa, a yanzu halin da suke ciki sai dai addu’a, domin akwai ‘yan uwansu da aka ce wai jirgi ma ya tafi ya bar su, abin da ya sa suka kasance a filin jirgin saman kara zube.
Ya ce “A yanzu suna kiranmu mu da muke a birnin Makka a kanmu kai musu agaji, don hatta abincin da za mu ci da ruwan sha ma babu shi a filin jirgin nan yanzu haka makewayin wajen ma maleji suke saboda tsabar cunkoson mutane .
Alfijr
Alhajin ya ce, su a yanzu agent dinsu ma yace kada suje ko ina su zauna a Makka har sai al’amura sun dai-daita a filin jirgin saman.
To sai dai kuma kakakin kamfanin sufurin jiragen sama na MaxAir, daya daga kamfanonin da dakatarwar ta shafa Ibrahim Dahiru, ya shaida wa BBC cewa, ba jiragen Najeriya ne kadai wannan mataki ya shafa ba, kusan jiragen kasashen duniya ne abin ya shafa.
Alfijr
Ya ce, hukumomin Saudiyya sun kafa wannan doka ce saboda cunkoson jirage bangaren tashin matafiya na filin jirgin.
Ibrahim Dahiru ya ce sakamakon wannan mataki hukumar kula da alhazai ta Saudiyya ta yi adalci wajen bayar da umarni a kwashe mutanen da ake ganin ba za a iya kwashesu zuwa kasashensu a cikin kwana daya zuwa biyu ba a kai su otel su zauna har sai an warware matsalar wato sai an kwashe wadanda ke kan layi tukunna.
Alfijr
Ya kara da cewar muna bin tsarin komawa da alhazai gidana ne domin akwai abin da ake kira ‘slot’, za a baka lambar slot dinka da lokacin da zaka kawo jirgi da kuma lokacin da zai tashi, don haka mu bamu saba ka’ida ba, haka suma sauran jiragen duniya suna bin wannan tsari ne.
To cunkoson jiragen da aka samu ne ya janyo wannan matsalar, kuma dama lokaci-lokaci ana samun irin haka, in ji shi.
Alfijr
Ya ce domin kokarin warware cunkoson jiragen ne hukumomin Saudiyya suka dauki wannan mataki, a don haka da sannu a hankali kowanne Alhaji da ya yi aikin Umrah zai koma gida.