Alfijr
Alfijr ta rawaito wasu Musulmi a Jihar Sokoto sun gudanar da Sallar Idi a ranar Lahadi, sun ki bi umarnin Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, wanda ya ayyana ranar Litinin a matsayin Idin karamar Sallah.
A ranar Asabar din da ta gabata ne Sarkin Musulmi wanda shi ne shugaban daukacin Musulmin Najeriya ya sanar da cewa ba a ga jinjirin watan Shawwal na shekara ta 1443AH ba.
Musulmin wadanda akasarinsu mabiyan Sheikh Musa Lukwa ne sun gudanar da Sallar Idi da misalin karfe 8 na safiyar Lahadi.
Alfijr
Da yake zantawa da jaridar Aminiya, Sheikh Lukkwa ya ce sun samu sahihin rahoto kan ganin watan a wasu sassan Najeriya da ma wajen kasar ne.
A cewarsa, an ga watan ne a jihohi biyar na Jamhuriyar Nijar, inda ya kara da cewa, “Na ga faifan bidiyo na shugaban kasarsu yana ayyana ranar Lahadi a matsayin ranar Sallah.
Kuma an ga watan a kasashen Afganistan da Mali da kuma kasashen Afrika da dama kuma sun gudanar da Sallar Idi a yau.
Alfijr
“Ko a Sakkwato ma an ga watan ne a wata al’umma da ake kira Fakku da ke karamar hukumar Kebbe da mutum takwas ciki har da babban limamin unguwar.
Kuma mutane 50 ne suka tabbatar da ganin jinjirin wata a kauyen Wauru da ke karamar hukumar Gada ta jihar.”