Yayin Neman Tsallakawa ƙasar Turai Maza Fiye Da 500 Ne Suka Yi Lalata Da Ni Bisa Tursasawa

Alfijr ta rawaito wata mata mai suna Maghnia da ke kasar Aljeriya ta bayyana cewar har da wadanda suke da cutar HIV, wasu ma sun mutu a kan idanunmu”.

Alfijr Labarai

Wata matashiya ‘yan asalin Najeriya ta tuna irin cin zarafi da wahalhalun da ta fuskanta a kan hanyarta ta tafiya nahiyar Turai domin kwadago.

BBC tace Mun sakaya sunan wannan matashiya muka sa mata suna Ada saboda wannan labarin.

Matashiyar tace ta fada tarkon masu safarar mutane ne a 2016, lokacin tana ‘yar shekara 20.

Ta kuma bayyana cewar sana ar gyaran gashi take yi a Jihar Delta, kuma mutumin da ya yi mata daɗin bakin cewa yana da ‘yar uwa da take gyaran gashi a Turai, kuma Turawan suna son yadda ‘yan Najeriya suke yaran gashi sosai.

Alfijr Labarai

Wannan shi ne asalin abin da ya sanya Ada barin gida, da zummar za ta je Turai kai-tsaye domin ci gaba da sana’ar da take yi a Najeriya.

Amma ta kwana da sanin cewa hanyar kasa za su bi su tafi ba jirgi za su hau ba, domin kuwa ko fasfo ba ta da shi.

An zuba mu a cikin motar Awaki daga ƙasar Nijar.

Mun hadu da masu bincike cikin sahara aka ce musu tinkiyoyi ne mu ba mutane ba, aka lullube mu da tamfol.”

“Daga Nijar muka bi cikin ruwa, kuma mun bi rana, mun shiga sahara kuma mun kusa wata guda cikinta.

“Wani buzu ne ya kwashe mu a motarsa, muka dauki hanya ban da tsayin kwana da tuni na mutu a wannan saharar, motar da muka shiga muna da yawa mun kai 20 maza da mata a kwance a but din motar.”

Alfijr Labarai

“A kwance muke kafada-da-kafada, wasu mutane da ke cikin saharan sun tsayar da mu, suka tambayi direban su waye a cikin motar, direban ya ce tinkiyoyi ne a ciki, a raina na ce ‘ohh wai ni ce tinkiya.’”

“Da yake motar a lillube take da tamfol, sai suka ce a cire shi su gani, kamar shi buzun da ya dauko mu yana da asiri a jikin zobensa, yana mirzá zoben sai ya bude ga mu dai a ciki amma tinkiyoyi suke gani,” in ji Ada .

Ada ta ce a karshe sun samu shiga Aljeriya zuwa wani gari da ake kira Oran, ta sake bayyana cewar cikin wadanda suka dinga tirsasani sun lalata dani har da masu cutar kanjamau

Bayan zamana a Algeria daga nan aka kai ni Morocco, sai na nemi na kama gabana a Casablanca, sai aka ce ai ba ni da ‘yancin tafiya saboda ana bi na bashi matar da ta biya kudi aka yi jigila da ni daga Najeriya zuwa nan.”

Alfijr Labarai

“Dirham D30,000 kwatankwacin yuro €4,000 ake nema daga hannuna, sune kudin jigilar, ba ni da yadda zan yi na sami wadannan kudin, don haka ba ni da wani zabi sai dai na yi karuwanci”, in ji Ada.

Farashi aka yi wa matan gidan na bai daya kuma ita mai lura da su tana rubuta yawan maza da kudin da yarinya ke samu, idan takai iyakar abin da za ta biya shikenan sai ta sallame ta.

Sai da Ada ta yi zaman gidan na kusan shekara biyu da rabi kan ta iya biyan kudin da ake binta.

Ta ce idan za a kwana D300 ake bya idan kuma kwanciyar ta dan lokaci ce D200 ne, kuma ko kwana mutum ya biya, sai kwanta da ita ne sau biyu kacal a daren.

Alfijr Labarai

A karshe dai Ada ba ta iya kai wa inda take so ta je ba, kuma a inda ta makale ba ta samun abin da za ta koma gida da shi ta nuna a matsayin ribar tafiyarta.

Sannan gudun jin kunya ka iya sa ta ci gaba da zama a nan, a gefe guda kuma cin zarafin da aka yi ta abu ne da ba zai taba gushewa ba a cikin ruhinta ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

BBC HAUSA

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *