Rundunar ’Yan sandan jihar Kano ta kama wata mata mai suna Maryam Usman mai shekaru 32 bisa zargin banka wa ɗakin kishiyarta wuta a unguwar Mangwarori da ke Mariri a Kano, lamarin da ya jikkata mutum huɗu.
A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ranar 13 ga Mayu, 2026, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:40 na dare a ranar 12 ga Mayu, bayan samun rahoton gaggawa cewa matar ta banka wa ɗakin kishiyarta Firdausi Saminu mai shekaru 40 wuta.
Sanarwar ta ce mutanen da suka samu raunuka sakamakon gobarar sun haɗa da Firdausi Saminu, da wasu yara biyu Isma’il Saminu mai shekaru uku da Khadija Saminu mai shekaru biyar, da kuma mijinsu Saminu Miko.
An bayyana cewa an garzaya da dukkan waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Kwararru na Sir Sunusi da ke Kano domin samun kulawa.
Rundunar ta ce jami’an sintiri sun isa wurin da gaggawa tare da cafke wacce ake zargin a wurin da lamarin ya faru, kuma yanzu haka tana tsare a ofishin ’yansanda na Mariri yayin da ake ci gaba da bincike.
’Yansandan sun ce za a miƙa shari’ar zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na jihar da ke Bompai domin gudanar da cikakken bincike kafin gurfanar da wacce ake zargin a kotu bisa tuhume-tuhumen ƙona gida da kuma yunƙurin kisan kai.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t