Ɗan China Ya Musanta Kashe Ummita A Kano, Yace Kalan Sharri Ne Kawai,

Alfijr ta rawaito bayan gurfana a yau Alhamis gaban mai shari’a, Dan China da ake zargi da kisan Bazawararsa Ummukhulsum (Ummita) a Jihar Kano ya musanta tuhumar da ake yi masa.

Alfijr Labarai

Mista Geng Quangrong ya musanta zargin, bayan karanto masa ƙunshin tuhume tuhumen da ake da ya ce ba gaskiya ba ne.

Mista Guo Cunru, shi ne mutumin da

Mista Gua Cunru ne don ya yi wa wanda ake zargin tafinta daga turancin Ingilishi zuwa harshen China.

kwamishinan Shari’a na Kano, Musa Abdullahi-Lawan, wanda shine lauya mai kare Marigayiya ya bukaci kotun ta fara sauraren tuhumar da ake yi wa wanda ake zargin don ba zasu bata lokaci ba a wannan shari’ar.

Ya kuma tabbatar da cewar wannan shari’ar ba zata wuce wata daya ba ta dade da yawa wata biyu, kamar yadda ya sanarwa freedom radio.

Alfijr Labarai

Mai Shari’a Sanusi Ado-Ma’aji ya ɗage shari’ar zuwa ranar 16 ga Nuwamban 2022 don gabatar da shaidun da masu kara.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *