Ƴan Sanda Sun Ceto Mutun 14 Bayan Kwashe Kwanaki 68 Hannun Ƴan Bindiga

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Alfijr ta rawaito rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara sun sami nasarar ceto mutane 14 da aka yi garkuwa da su, bayan sun kwashe kwanaki 68 a sansanin ‘yan bindiga.

Hakan yana fito ne daga bakin Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu lokacin da ya ba je kolin mutanen ga manema labarai a shalkwatar Hukumar da ke Gusau Babban birnin Jihar, ya ce, jami’an ‘yan sanda tare da ‘yan banga ne suka ceto wadanda lamarin ya rutsa da su, a lokacin da suka Kai wani samame a dajin Munhaye da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.

Ya kara da cewa Jami ansu tare da ‘yan banga, yayin da suke gudanar da wani samame sun yi nasarar fatattakar wasu ‘yan bindiga a sansanin ‘yan fashin mai suna “Dogo Sule”.

Ya ce” An ceto mutane 14 da aka yi garkuwa da su, wadanda suka hada da manya maza biyu, mata bakwai da yara biyar ‘masu kasa da shekaru biyu.”

Shehu ya ci gaba da cewa, a yayin zantawa da wadanda abin ya shafa, sun sanar da jami’an ‘yan sanda cewa, a ranar 1 ga watan Janairu, 2023, da misalin karfe 1 na dare, wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan fashi ne dauke da manyan makamai sun kai farmaki a kauyukan Anguwar Mangoro da Gidan Maidawa.

Shehu yace, “Wadanda abin ya shafa an kai su asibitin ‘yan sanda da ke Gusau domin kula da lafiyarsu, daga nan kuma aka sake mika su ga iyalansu da ‘yan uwansu.

Shugaban Rundunar ‘yan sandan jihar CP Kolo Yusuf ya taya wadanda lamarin ya rutsa da su murnar samun ‘yancinsu, da fatan Allah ya kare gaba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *