Jam’iyyar APC ta yi nasara a zaɓen cike gurbi na Ghari/Tsanyawa da aka gudanar a jihar Kano.
Da yake bayyana sakamakon zaɓen da misalin ƙarfe 6:10 na safiyar Lahadi, jami’in tattara sakamakon zaɓen, Farfesa Muhammad Waziri daga Jami’ar Bayero, ya sanar da cewa Garba Ya’u Gwarmai na jam’iyyar APC ya yi nasara da ƙuri’u 31,472.
Ya doke ɗan takarar jam’iyyar NNPP, Yusuf Ali Maigado, wanda ya samu ƙuri’u 27,931.
An gudanar da zaɓen cike gurbin ne bayan an bayyana zaɓen farko da aka yi a mazabar a matsayin wanda bai kammalu ba.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t