Alfijr

Alfijr
Innalillahi wa inna ilaihirraji un, Allah Ya yi wa mahaifin Singham tsohon kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano Alhaji Buba Turaki, rasuwa da safiyar ranar Lahadi a Jihar Gombe.
Alhaji Buba ya rasu yana da shekara 106 a duniya, shi ne mahaifin tsohon CP Muhammad Wakili da ake yi wa lakabi da Singam na Kano.
Alfijr
Ya rasu ya bar matan aure da ’ya’ya 10, maza 5 da mata 5, an gudanar da jana’izarsa da misalin karfe 2 na rana a kofar Fadar mai martaba Sarkin Gombe.
Allah ya gafarta masa Allah ya shafe kura kuransa da sauran Al ummar Annabinmu.