Dubun Wasu Tarin ‘Yan Yahoo Boys Ta Cika

Alfijr

Alfijr ta rawaito, jami’an ‘yan sandan babban birnin tarayya sun kai sumame wani a unguwar Gwarinpa Mab Global Estate da ke babban birnin tarayya Abuja, in da ake zargin ‘yan damfara ne na yanar gizo, wadanda aka fi sani da Yaboo boys suka mamaye gidan.

Alfijr

Jaridar Punch ta ruwaito cewa wadanda ake zargin sun kai kimanin mutum 40, sun mamaye gidan ne a ranar Asabar, sanye da fararen kaya ne.

Wani mazaunin unguwar ya shaida wa wakilinmu a ranar Talata cewa, wanda ake zargin ya ce an dauke su ne domin yi musu tambayoyi a ranar Litinin.

Alfijr

Majiyar ta ce, “’Yan sanda sun zo ne a jiya Litinin domin su gano ainihin abin da ya faru a daren.

Jami’an tsaro sun bukaci yin magana da mamallakin gidan da ake zargin yaran Yahoo suna ciki, Sun tafi da ita don ƙarin tambayoyi. Kamar yadda nake magana da ku, har yanzu tana hannun ‘yan sanda. Inji ganau din

Alfijr

Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan birnin tarayya , DSP, Josephine Adeh, bayan da muka tuntube ta akan lamarin mun kasa samun jin ta bakinta a kiran wayar da aka yi mata.

Har ila yau, ba ta mayar da martani ga sakon da aka aika wa layinta kan lamarin ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.