Kotu Ta Daure Wani Dattijon Biri , Bayan Da Ya Yiwa Yarinya ‘Yar shekara 14 Ciki, Da Yunkurin Zubar Da Cikin

Alfijr

Alfijr ta rawaito, wani mutum mai shekaru 45 mai suna Rufus Olatunji, mai shari’a ya aike da shi gidan gyaran hali da tarbiyya bisa zarginsa da yi wa wata yarinya ‘yar shekara 14 fyade tare da yi mata ciki a harabar cocin Royal World Embassy Church da ke Ipaja a karamar hukumar Alimosho a Lagos.

Alfijr

Ana zargin Olatunji da lalata yarinyar tsawon watanni da dama kafin ta dauki ciki.

Wanda ake zargin, an gurfanar da shi a ranar Talata a gaban wata kotun majistare ta Ebute Meta, an kuma ce ya bai wa karamar yarinya wata kwaya ne a yunkurin zubar da cikin.

Alfijr

Ya yi barazanar cewa zai daina hulda da ita, idan ba ta sha wannan kwayar ba.

A wani bangare na tuhumar, an ce kai Rufus Olatunji, wani lokaci a cikin watan Agusta 2021, a harabar cocin Royal World Embassy Church, Ipaja, ka aikata lalata da yarinya ba bisa ka’ida ba, yar shekara 14 da haihuwa, ka kuma bata miyagun kwayoyi da nufin ta zubar da ciki, aikata laifin da za a hukunta shi a karkashin sashe na 145(1) na dokar laifuka ta jihar Lagos 2015.”

Alfijr

Dan sanda mai shigar da kara, Olatunde Kehinde, ya bukaci kotun da ta tasa keyar wanda ake kara zuwa gidan gyaran hali da tarbiyya

Alkalin kotun, Misis Alani Kayode, ta amince da bukatar sannan ta dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 8 ga Maris, 2022, domin yi masa shari’a.

Slide Up
x