Alfijr
Alfijr ta rawaito, an kama wani malamin makarantar firamare mai suna Mukaila Abdurrazak bisa zarginsa da lalata da dalibarsa mai shekaru 13 da haihuwa. a jihar Zamfara.
Wata sanarwa da kakakin rundunar hukumar NSCDC ya fitar a ranar TALATA, Mista Ikor Oche, ya bayyana cewa matashin mai shekaru 30 da haihuwa yana amfani da damar da ya samu wajen koya wa yarinyar a gida da kuma makarantarta dake Gusau.
Alfijr
A nasa bangaren wanda ake zargin ya amsa laifinsa ne a lokacin da ake gudanar da bincike na farko.
Hukumar tace za ta kammala bincike don gurfanar da shi a gaban kotu don ya girbi abinda ya shuka.
Alfijr
Kamar yadda Crimechannels ta rawaito