An Saka Bom A Gidan Kallon Ball A Garin Kaduna

Alfijr

Alfijr ta rawaito, an gano bom din ne bayan wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar ranar Lahadi tana gargadin ’yan jihar game da shirin ’yan ta’adda na cewar zasu saka bama-bamai a makarantu da asibitoci da wuraren ibada da sauran wuraren taruwan jama’a.

Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida ta jihar ta yi gargadin ne bayan fashewar wani bom a kangon wani tsohon otal da ke unguwar Kabala a jahar Kaduna.

Alfijr

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta ce ta samu rahoton wani abun fashewa ne a ranar Talata, a gidan kallon kwallon kafa da ke otal din Larry Breeze Bar.

Yan sandan sun kara da cewa, bisa bayanan da muka samu ne muka tura jami’an Sashen Kwararru kan abubuwan masu fashewa nan take, suka je suka kwance bom din cikin nasara,” inji, ASP Mohammed Jalige.

Alfijr

Jalige ya shawarci al’ummar jihar da su ci gaba da lura da abubuwa da ke faruwa a zagayensu tare da kai rahoton duk abun da ba su yarda da shi ba ga jami’an tsaro a kan lokaci.

A cewarsa, “Tuni aka fara bincike game da bama-baman biyu domin cafko wadanda suka dasa su da nufin jefa al’umma cikin zullumi.

Alfijr

Kamar yadda jaridar Aminiya ta rawaito

Slide Up
x