An Kashe Mutane Goma Sha Takwas 18, A Wani Hari Da Ake Kyautata Zaton Makiyaya Ne

Alfijr ta rawaito an kashe mutane goma sha takwas 18, a wani harin da ake kyautata zaton makiyaya ne a ranar Alhamis din da ta gabata.

Maharan sun mamaye wasu kauyuka hudu a karamar hukumar Guma ta jihar Benue inda suka kashe mutane 18 tare da jikkata wasu da dama.

A cewar ‘yan asalin yankin, an ce wadanda ake zargin makiyaya ne sun afkawa kauyen Ukohol ne a lokacin cin wata kasuwa.

An tattaro cewa lokacin da aka yi wa makiyayan a Ukohol, sai suka koma yankunan da ke kusa.

Shugaban karamar hukumar Guma Mike Ubah ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya kara da cewa an kashe mutane 18.

Da yake zantawa da manema labarai a ranar Juma’a, shugaban ya ce, “Makiyaya dauke da makamai sun far wa jama’ata a Ukohol, inda suka kashe mutane a kalla 10.

Mafi munin lamarin shi ne har sun kashe yara ‘yan kasa da shekara biyu.

“Ba su tsaya a lokacin ba sai suka je kauyuka uku/mazauna a kusa da su, suka kashe wasu takwas, jimillarsu 18, goma a kasuwa, takwas a kauyuka lokacin da su (makiyaya) suke dawowa.

Ranar kasuwa ce, sai suka je can suka fara harbi.

Abin da ke faruwa a yanzu shi ne yadda suke kokarin tada zaune tsaye daga kauyuka da matsugunan al’umma da suka mamaye su da kiwo cikin dare.

“Makiyayan sun bayyana sanye da bakaken kaya a jikinsu.

Babu wani kauye da ya tsira kuma daukacin kananan hukumomin Guma 10 abin ya shafa,” in ji shugaban karamar hukumar.

Lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Catherine Anene, ta ce, “An tabbatar da faruwar lamarin amma har yanzu babu cikakken bayani”.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *