Gwamna Ganduje Ya Gabatar Da Kasafin Kudin 2023 Ga Majalisar Dokokin Jihar Kano

Alfijr ta rawaito Gwamna Abdullahi Ganduje ya gabatar da kasafin Naira biliyan 245 na kasafin shekara ta 2023 ga majalisar dokokin jihar domin amincewa da shi.

Da yake gabatar da kudirin mai taken “Budget of Consolidation and Prosperity II” a ranar Juma’a a Kano, Gwamna Ganduje ya ce an yi hakan ne domin karfafawa tare da inganta rayuwar al’ummar jihar.

Ya ce kasafin ya kunshi Naira biliyan 144 na manyan ayyuka, wanda ya nuna kashi 59 cikin 100 da kuma Naira biliyan 100 na kudaden da ake kashewa akai-akai, wanda ya nuna kashi 41 cikin 100.

An ware wa fannin lafiya Naira biliyan 39.1; albarkatun ruwa Naira biliyan 15; fannin sufuri Naira biliyan 8.6; fannin noma Naira biliyan 19.9 yayin da ayyuka da ababen more rayuwa suka samu Naira biliyan 35,” inji shi.

Gwamnan ya ce bangaren ilimi ya samu kaso mai dadi na kasafin kudi da Naira biliyan 62, wanda ya kai kashi 27 cikin 100 fiye da shawarar UNESCO da Majalisar Dinkin Duniya.

Ya Kara da cewar za a fitar da kudaden ne wajen aiwatar da manufofi da tsare-tsare da nufin tabbatar da ingantaccen ilimi a dukkan matakai.

Gwamna Ganduje ya ce za a kuma yi amfani da wani bangare na kudaden wajen inganta shirin ilimi kyauta da na dole a jihar.

Ganduje ya bukaci ‘yan majalisar su tabbatar da a gaggauta amincewa da kasafin kudin, domin baiwa gwamnati damar ci gaba da samar da ribar dimokuradiyya ga mutane.

Hakazalika ya kuma bukaci matasa da su guji duk wani nau’in tashin hankali, musamman ganin zaben 2023 ya gabato.

Shugaban majalisar, Hamisu Chidari, ya baiwa gwamnan tabbacin yin gaggawar zartar da kasafin kudin domin samar da lokacin da’irar kasafin kudin watan Janairu zuwa Disamba.

Ya bukaci ma’aikatun gwamnati, ma’aikatun da hukumomi , MDAs, da su kasance a shirye don kare kasafin kudi a majalisar.

Kakakin majalisar ya kuma yabawa gwamnan bisa kokarin da yake yi a bangaren samar da ababen more rayuwa, tsaro, lafiya da ilimi a fadin jihar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *