Daga A’isha Salisu Ishaq
Rahotanni daga jihar Katsina na cewa jirgin yaƙin sojin Najeriya ya kashe mutum shida bisa ‘kuskure’ a lokacin da sojojin ke bin wani gungun masu garkuwa da mutane.
Alfijir labarai ta rawaito cewa mazauna ƙauyen Zakka a Katsina sun ce jirgin sojin sun jefa bama-bamai a kan rukunun bukkoki, abin da ya janyo sanadiyyar kisan mutum shida.
Luguden wutar kamar yadda wani rahoto ya ce na zuwa ne bayan da wasu yan bindiga sun kai wa wani sansanin Yan sanda hari in da suka kashe jami’an guda biyu da ɗan sinitiri guda ɗaya.
Sai dai ƙungiyar Amnestiy International ta nemi da a gudanar da bincike.
Har kawo yanzu sojojin Najeriya ba su ce uffan ba dangane da harin na ‘kuskure’.
A baya dai sun sha bayyana cewa hare-hare irin waɗannan na kuskure ne, kuma za a ɗauki matakan kawo ƙarshen afkuwar hakan a gaba.
Wannan ne dai karo na 10 da ake samun irin waɗannan hare-hare na kuskure a shekaru biyu sannan na 11 a tsawon shekaru takwas.
Ko a watan Janairun 2025 ma sai da aka samu irin wannan harin na kuskure a a jihar Zamfara inda fafaren hula 16 suka mutu.
A watan Disamban 2024 ma an samu irin wannan hari a jihar Sokoto wanda ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula 10.
BBC
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ