Ana Zargin Alƙali Aminu Gabari Na kotun No-man’s-land Kano da Karɓar Cin Hanci

Alfijr

Alfijr ta rawaito Cibiyar wayar da kan al’umma kan shari’a da bin diddigin al’amura (CAJA) ta rubuta koke a kan babban alkalin jihar Kano bisa rashin daukar matakin ladabtarwa a kan Alkali Aminu Gabari bisa zarginsa da cin hanci da rashawa.

Karar mai dauke da kwanan watan 15 ga watan Maris, Kabiru Sa’id Dakata ne ya sanya wa hannu, kuma ta mika wa alkalin alkalan Najeriya kuma shugaban majalisar shari’a ta kasa, Justice Tanko Muhammad.

Cibiyar wayar da kan al’umma akan shugabanci nagari da tabbatar da adalci wato CAJA ƙarƙashin jagorancin Comrade Kabir Dakata ta miƙa koke ga babban joji na ƙasa kan zargin Alƙalin Kotun Majistiri Aminu Gabari akan muzgunawa ƴan adawar siyasa.

Alfijr

Takardar ta ce CAJA ta lura bayan binciken da ta yi na cewa, duk da cewa akwai alkalai sama da 80, manyan magatakardar babbar kotun jihar Kano na da dabi’ar da za su jagoranci duk wasu shari’o’in da aka fallasa a siyasance da suka shafi Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ko kuma duk wani dan jam’iyya mai mulki, a kan duk wani dan adawar siyasa, ga wani babban Alkali Aminu Muhammad Gabari na kotun majistare mai lamba 58, Nomansland, Kano.

Alfijr

Ga cikakken bayanin nan a takardu

Slide Up
x