Gwamnatin Tarayya Ta Tabbatar Da Janye Tallafin N600bn na Wutar Lantarki

Alfijr

Alfijr ta rawaito hukuma mai kula da harkar wutar lantarki a Najeriya, Nigerian Electricity Regulatory Commission ta ce gwamnatin tarayya ta janye tallafin wuta.

Hukumar NERC a ranar Laraba ta na cewa tallafin shan wutan da ya ci wa gwamnatin tarayya N600bn ya zo karshe a halin yanzu.

NERC ta bada sanarwar kara farashin shan wutar lantarki a Fubrairun wannan shekara ta 2022, an dauki wannan mataki ba tare da wani bata lokaci ba.

Alfijr

Hakan na zuwa ne a lokacin da kamfanonin da ke samar da wuta su ka soki aikin NBET, suka ce kamfanin ya gagara yin abin da ya dace na biyansu kudinsu.

Garba ya ce aikin NERC shi ne tsaida farashin da masu shan wuta za su biya, hakan ya na nufin hukumar ta na shiga tsakanin kamfanonin wuta da customers dinta.

Alfijr

A ranar 1 ga watan Fubrairun 2022 aka samu sauyin farashi a kasar nan. NERC ta ce duk bayan watanni shida ya kamata farashin wuta ya canza a kasuwa.

Farashin yana canzawa ne sakamakon canjin kudin kasar waje da tsadar kaya a kasuwa.

A ranar Talata, tashar watsa wuta ta kasa ta yi gobara, sa’o’i kadan bayan da aka maido da ita bayan ta sami matsala a ranar Litinin, wannan dai shi ne karo na uku a bana kuma karo na shida a cikin shekarar da ta gabata.

Alfijr

Rikicin bangaren wutar lantarki ya kara kamari. Lokaci ya yi da shugaba Muhammadu Buhari ya amince da gazawarsa wajen farfado da ita, ya tara jihohi 36, kamfanoni masu zaman kansu da kuma abokan ci gaban kasa da kasa don tsara shirin ceton gaggawa.

Kamar yadda jaridar PUNCH ta ruwaito

Slide Up
x