Asma’u Sadik (Baby Nayis) Ta Zama Sarauniyar Mawaƙan Matan Arewacin Najeriya

Alfijr

Alfijr ta rawaito Abdullahi Yalwa Ajiyan Yawuri, wanda shine dhugaban ƙungiyar masu kafafen yaɗa labarai ta Arewacin Najeriya, ya ce, ƙara buɗe kafafen yaɗa labarai kan ƙara samar da ci gaba a tsakanin al’umma.

Alfijr

AjiyanYawuri ya bayyana hakan ne, a yayin taron liyafar cin abinci da girmama wasu daga cikin kafafen yaɗa labarai da kuma wasu mawaƙa a Arewacin Najeriya, wanda ya gudana daren Lahadi a wani ɗakin taro dake kan titin Jami ar Bayero ta Kano.

Asma’u Sadik wadda aka fi sani da Baby Nayis na daga cikin waɗanda a ka baiwa lambar yabo a matsayin sarauniyar mawaƙan matan Arewacin Najeriya.

Alfijr

Baby Nayis shahararriyar mawakiyar gada, kuma yanzu haka itace, shugabar sashin shirye-shiryen tashar Dala FM Kano,

wa

Bayan godiya ga Allah da tayi na wannan karramawar da aka mata, ta kuma waƙe ƙungiyar a wajen taron, sannan ta ce, karramawar da a ka yi mata zai ƙara mata ƙwarin gwiwa wajen gudanar da ayyukanta na yau da gobe kamar yadda ta saba.

Slide Up
x