Atiku Abubakar Ya Kaddamar Da Wani Sashe A Maaun Kano Mai Dauke Da Sunansa


Alfijr ta rawaito Wazirin Adamawa, Alhaji Atiku Abubakar tare da rakiyar wasu jiga-jigan ajin farko da a jam iyyar PDP, suka kai ziyarar bude wani Katafaren sashe a MAAUN Kano.

Alfijr Labarai

Atiku ya samu rakiyar Ifeanyi Okowa da Gwamnan jihar Delta, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal, Gwamnan jihar Sokoto, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule. Lamido, Sanata Mal Ibrahim Shekarau, Sanata Dino Malaye, Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa, Iyorchia Ayu, tare da wasu manyan baki sun ziyarci babbar jami’ar Maryam Abacha American University of Nigeria MAAUN, a  Jihar Kano,.

Maaun Kano

Ziyarar da ta zamo ta tarihi ta kasance, inda suka kaddamar da Sashen. Kimiyyar Zamantakewa da Gudanarwa, (SCHOOL OF SOCIAL AND MANAGEMENT SCIENCES)
wadda aka sanyawa sunan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Alh Atiku Abubakar, wanda aka gudanar a MAAUN jihar Kano da safiyar yau.

Alfijr Labarai

Wazirin Adamawa ya samu babbar tarba daga wanda ya kafa MAAUN Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo da  shugaban makarantar, Farfesa (Dr.) Mohammad Israr da sauran manyan jami’an gudanarwa na Jami’ar.

Maaun Kano

Alhaji Atiku cikin farin ciki ya nuna jin dadinsa tare da addu’ar samun nasara ga daukacin Malamai da Dalibai da Jami’a baki daya.

Maaun kano

Alhaji Atiku ya kuma yabawa wanda ya assasa Jami’ar Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo bisa gagarimar kafa daular ilimi mai daraja ta daya a Afirka.

Slide Up
x