Shugaba Bola Tinubu ya bukaci babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da karar da ke neman tilastawa majalisar dokokin kasar fara yunƙurin tsige shi bisa zargin take hakkin ƴan ƙasa.
Alfijir labarai ta rawaito Lauya mai suna Olukoya Ogungbeje ne ya shigar da karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1334/2024 a gaban kotun.
Mai shigar da karar, a cikin karar da ya shigar da ta hada da Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Prince Lateef Fagbemi, SAN, a matsayin wanda ake kara na 2, na neman kotu ta saurari korafe-korafen sa guda shida.
Ya bukaci kotun da ta bayyana cewa ci gaba da murkushe zanga-zangar lumana da ‘yan Najeriya suka shirya, da gwamnatin shugaba Tinubu ta yi, laifi ne da ba zai iya sanya wa a tsige shi a matsayin shugaban kasa.
Sai dai, a wani martani na farko na hadin gwiwa da suka shigar a kan karar, Shugaba Tinubu da AGF sun ƙalubalanci hakascin mai ƙarar ya shigar da karar.
Baya ga rokon kotun da ta yi watsi da karar saboda rashin cancanta, wadanda ake tuhumar sun dage cewa matakin ya kasa bayyana dalilin da ya dace na daukar matakin da zai ba shi damar yin hukunci a kansa.
A halin da ake ciki, Mai Shari’a James Omotosho, a jiya Litinin, ya dage ci gaba da shari’ar har zuwa ranar 4 ga watan Maris domin baiwa lauyan da ke wakiltar mai kara, Mista Stanley Okonmah damar mayar da martani kan matakin farko na shugaba Tinubu da AGF.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ