Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Mai Girma Gwamnan Kano Ganduje – Kwamared Sani Tela

Alfijr ta rawaito Kwamared Sani Bala Tela bayan zungureriyar wasika da ya aikowa Mawaki Rarara kan danbarwarsa da Gwamna Ganduje, yanzu haka ya sake aikowa mai girma Gwamna

Alfijr Labarai

Tela ya fara da sallama irin addinin Musulunci, ya kara da cewa ina maka gaisuwa tare da girmamawa a matsayinka na Kaka,Uba, kuma shugabana

Na rubuto maka wannan wasika ne a matsayina na talakanka a jihar Kano mai bada yar gudummawar sa don ganin duk abunda zai sa a samu cigaba kuma a kauda matsaloli a Kano.

Ya ƙara da cewar nayi rubutun nan ne dangane da wata yar takaddama da ke faruwa tsakaninka da Ɗanka ko jikanka (RARARA)

Maigirma Gwamna duk wanda a kace shugabane musamman ma a gari irin Kano wadda ake wa lakabi da karamar Nigeria, ai sai yaji bai jiba, ya gani bai gani ba.

Alfijr Labarai

Sani ya Kara da cewa mai girma gwamna banda zamanka gwamnan, zai wahala a tambayi wani mutum a Kano ya iya fadar abokin fadanka sabida hakurinka.

Muna kuma sane da irin takalarka da aka dinga yi a siyasance kafin zamanka gwamna, da hakkokinka da aka take duk bakayi komai ba akai ka hakura

Don haka kokarinka na taimako har khadimul Islam aka samaka, kuma jama’a da yawa sun shaida irin taimakon da kayi da kuma gudummawar da kabawa musulunci da musulmai iya gwargwado.

Mai girma gwamna yanzu fa idan za’a lissafa mutane masu shekaru a kano dole sai an hada da kai, domin an kwana biyu fah ga yaya, Jikoki da surukai. In Ji Tela

Alfijr Labarai

Kwamared ya kara da cewa idan maganar Administration ne kuma nan kana sahun ga ko a Nigeria za’a nemoka ka don ba’a zaka bamu kunya ba, kowa ya shaida wannan don ba inda baka kewaya ba a kasar.

Mai girma gwamna, yanzu fa a siyasa kai International ne, don haka bai kamata ka tsaya ana local Derby da kai ba, wannan bai dace da matsayin da Alla yayi maka da darajar da ya baka a cikin Al’umma ba.

Kuma a matsayinka na gogaggen Dan siyasa, na dauka kun gaya mana cewa cikar Dan siysa shine ya iya maida makiynsa masoyinsa, ya kuma iya rike masoyinsa da magoya bayansa.

Ina ganin ya kamata mai girma wannan wasan jika da kakan da kukeyi da RARARA a barshi haka don wasu sun shigo sun bata muku wasan ku kuna cikin daki baku sani ba kai da jikanka.

Alfijr Labarai

Hakazalika mai girma gwamna, ya kamata a tuna baya lokacin da shi wannan jika naka yake tare da kai ba irin zagi, wulakanci ,Cin mutuncin da asarar da bai yi ba sabida kai, kuma kaima kayi masa halasci iya gwargwado don nima shaida don jikan nan naka Makoci nane tsawon shekara 9, kuma bamu ta ba samun sabani ba har yau dinnan duk da na bar unguwar da muke zaune tare amma har yanzu iyalinsa suna zumunci da nawa.

Kark manta mai girma Gwamna .Kano karin hadin kai take bukata a yanzu ba rikici ba,

Musamman ma dai na siyasa domin ga zabe ya tunkaro mu sabida haka dole ne yanzu mu kula sosai don jihar nan tamu tana da kishiyoyi da yawa.

Alfijr Labarai

Mai girma Gwamna, Kayiwa Allah da Annabinsa sallallahu Alaihi wa sallam a dakatar da wannan matsala ko da baza ayi tafiya tare ba yana da kyau dai a daidaita in yaso Allah ya hada kowa da rabonsa.

A karshe ina fata zaka bawa mara ‘da kunya ka dubi wannan koke nawa

Daga Talakanka ,Danka kuma jikanka
Comrade Sani Bala Tela

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Slide Up
x

2 Replies to “Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Mai Girma Gwamnan Kano Ganduje – Kwamared Sani Tela

  1. Bazan gaji da maka korafin ka gyara rubutu ba a matsayina na bahaushe… wallahi da ace da turanci kake rubutun nan da abin kunya ya ishe mu.
    Babu wani labari da zaka wallafa ba tare da kurakurai ba. Musamman ma wajen spelling.

    GYARA KAYANKA

    1. Ina godiya sosai da kulawa Jamal
      Wallahi Ina jin daÉ—in yadda kake nuna damuwa ainin, don Allah kayi min shot din wajen domin na gyara.

      Allah ya sani ina duk yadda zan yi wajen kulawa, amma dake kasan marubuci makaho ne.

      Allah ya saka da alheri ameen

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *