Alfijr
Alfijr ta rawaito Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da kafa sabbin makarantu guda uku a sassa daban-daban na kasar nan.
Sanarwar da Daraktan hulda da jama’a na ma’aikatar ilimi ta tarayya Ben Goong ya fitar a ranar Talata, ta ce za a gina sabbin cibiyoyin ne a jihohin Kano da Abia da kuma Delta.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, a bisa kudirinsa na ganin an samu saukin karatun manyan makarantu, shugaban kasa Muhammadu Buhari (GCFR) ya amince da kafa sabuwar kwalejin fasaha ta gwamnatin tarayya guda uku a kasar nan.
Alfijr
Za a gina makarantun ne a Umunnoechi a jihar Abia, da Orogun a jihar Delta da kuma Kabo a jihar Kano.
A cewar Daraktan, sabbin Cibiyoyin za su fara ayyukan ilimi ne a watan Oktoba, 2022 wanda hakan ya kawo adadin makarantun gwamnatin tarayya zuwa talatin da shida a kasar, inda kowace jiha ke da daya daga cikin cibiyoyin.