Alfijr ta rawaito gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya amince da nadin sabon shugaban ma’aikata, Usman Bala Muhammad, wanda har zuwa sabon nadin nasa, ya kasance babban sakatare a ma’aikatar yada labarai.
Sauran manyan sakatarori da aka nada su ne Injiniya Muhammad Bello Shehu, wanda kafin ya kasance daraktan bincike da kididdiga na hukumar kula da hanyoyin Kano (KARMA), wanda yanzu ya zama sakatare na dindindin.
Wata sanarwa da Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan, Abba Anwar, ya fitar a ranar Litinin, ta ce Magaji Lawan, wanda shi ma har zuwa lokacin da aka nada shi a matsayin Babban Sakatare, shi ne babban Daraktan na Ma’aikatar Kudi.
Alfijr
Bilyaminu Gambo Zubairu, wanda kuma shi ne Darakta PHC. Ofishin Shiyya na Rano, yanzu ya zama sabon Sakatare na dindindin.
A cewar sanarwar, Mairo Audi Dambatta, wacce ta kasance Darakta a ofishin shugaban ma’aikata, yanzu ta zama Sakatare na dindindin.
Alfijr
A yayin da yake taya su murnar wannan sabon aikin da aka ba su, Gwamna Ganduje ya ji dadin yadda a kullum suke yin aiki tukuru domin inganta kyawawan dabi’u a aikin gwamnati.